
HausaRadio.net
By HausaRadio.net

HausaRadio.netMay 24, 2021

"Daga Laraba" 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao
Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao
Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka da yawan su, sun gwammace su yi hijira zuwa arewa.
Podcast Trailer: https://youtu.be/qzLb2V9521U

Komai muka samu mu fassara zuwa yaren mu Hausa - Malam Habibu Sani Babura
Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa a Jami'ar Bayero ta Kano.
Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna Firdausi).

#RanarHausa 2020-08-25 Arewa Radio 93.1's Program with BANNigeria
Shirin Arewa Radio kan #RanarHausa2020 tare da Faisal Abdullahi (@BANNigeria) da Mazhun (@HausaTranslator) na Bloggers Association of Northern Nigeria.

#RanarHausa 2020 - Shirin Daga Taskar Hausa Daga Guarantee Radio 94.7 Kano
Shirin Daga Taskar Hausa inda aka tattauna da Farfesa Aliyu Muhd Bunza da Dakta Abdulƙadir L Koguna da kuma Dakta Muhammad Suleiman A., a kan Ranar Hausa ta Duniya wato 26 ga watan Ogusta 2020.
Ku kasance da shirin a yau, Lahadi, ƙarfe 8 zuwa 9 na dare. Daga Guarantee Radio 94.7 Kano a ranar Lahadi Aug 23, 2020.
Za ku iya saurara kai tsaye daga ko'ina a www.guaranteeradio.com

Kaucewa #LabaranBogi (Stopping the spread of #FakeNews in Hausa media)
Kai tsaye acikin shirin #ZararBubu da @CDDWestAfrica ke daukar nauyin kawowa masu sauraro dan wayar da kai game da #LabaranBogi, Dr. Nura Ibrahim ke jawabi game da yadda za'a kaucewa labaran bogi a shafukan sada zumunta na zamani.
Related links:
https://twitter.com/CDDWestAfrica_H/status/1286959730716545026 https://youtu.be/aOgO9amMnl4#ADainaYadaLabaranKarya #ADenaYadaLabaranKarya #StopFakeNews #StopSpreadingFakeNews #FakeNews #HausaFakeNews #FakeHausaNews #LabaranBogi

Asalin Ranar Hausa 2015 - Shirin VOA Hausa na Yau Da Gobe
Jamila Kabiru Fagge da Bashir Ahmad sun tattauna akan #RanarHausa August 26, 2015
Originally released August 28, 2015 on https://www.voahausa.com/a/2918757.html and https://soundcloud.com/voahausa/yau-da-gobe-134.

DW Hausa - Taba ka Lashe - Tasirin Wasan Kwaikwayo 2020.05.28
DW Hausa - Taba ka Lashe - Tasirin Wasan Kwaikwayo 2020.05.28
Mai gabatarwa: Fauziyya Dauda

Hausa News Headlines - Kanun Labaran Hausa na 2020.05.08
Full transcript: http://hausadictionary.com/hausaradio/20200508
1 Kanun Labaran DW Hausa - Shirin Yamma 08.05.2020 2 Kanun Labaran VOA Hausa - Shirin Dare 2030 UTC (30:00) - Mayu 08, 2020 3 Kanun Labaran RFI Hausa 20h00 - 20h17 GMT - Labarai 08/05 20h00 GMT 4 Kanun Labaran Talabijin na BBC Hausa 08/05/2020 5 Kanun Labaran Radio VOH 3 - 20200508
BBC Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.22
Show notes and transcript <> Cikakken bayanin wannan podcast din: http://bit.ly/BBCHausaSafe20190522

RFI Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin 07h00 Asabar 2019.05.18
Host (mai gabatarwa): Abdullahi Isa
K'asashe masu k'arfin tattalin arziki da aka sani da G7 sun gudanar da taro a birnin Paris, taro da ya mayar da hankali zuwa ga batutuwan da suka shafi kiwon lafiya. Yayin da gwamnatin k'asar Venezuela da kuma 'yan adawa da ke cigaba da kai ruwa rana suka soma tattaunawa a Norway. Za ku ji cewa shafin sada zumunta na Facebook ya san da rusar wasu shafuka 216 na k'arya wadanda ake amfani da su domin rubuta kalamai ko kuma batutuwa da ba su dace ba zuwa wasu k'asashe. DRC: Gabbacin jamhuriyar demokradiyar Kongo a jiya Juma'a, har an fuskanci bori da ya kai ga rasa ran wani d'alibi mai shekaru sha biyu. Idan da sauran lokaci, da labaran wasanni (sports news). Read more at http://bit.ly/RFIHausa07h00Sat20190518
VOA Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17
Hosts (masu gabatarwa): Grace Alheri Abdu, Baba Yakubu Maƙeri
US: Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanar da wani sabon tsarin dokan bakin haure, wanda zai [unintelligible] gurbin baki d’ayan dokan bakin haure a nan Amurka. US: A wata sabuwa kuma Donald Trump ya ce yana k'ir da zaton Amurka ba za ta shiga da yak'i a Iran ba a lokacin da ake k'ara samun tankiya a gabas ta tsakiya. Burkina Faso: Bayan haka, ministan harkokin wajen Burkina Faso ya yi kira ga k'asashen duniya su kafa wata had'akar yak'i da ayyukan ta'addaci kamar irin wadanda aka kafa su a k'asashen Iran da Afghanistan domin yak'i a yankin Sahel... Read more at http://bit.ly/VOAHausaSafe20190517
BBC Hausa News Headlines Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17
Host Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baffa
"Farko, mutum ya zama cewa yana yawan motsa jiki. Sannan kuma a … Read More at http://bit.ly/BBCHausaSafe20190517
Thank you for subscribing. Share this episode.

DW Hausa Shirin Safe na 2019-03-01
Masana tattalin arziki da hada-hadar kudi a Najeriya, sun bada shawarar cewa ya kamata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta bada himma wajen raya tattalin arzikin kasar musamman a yankin arewacinta domin magance matsalolin da ke addabar yankin.
Hosts: Muntaqa Ahiwa Nigeria: Cikin shirin za'a ji yadda masana suka soma baiwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shawara kan buƙatar zaburar da harkokin tattalin arziƙi, musamman ma na arewacin ƙasar da ke fama da matsaloli. Cameroon: Yara ne da ke fama da cutar nan ta HIV mai karya garkuwar jiki da ke cikin mummunar yanayi na rashin maganin rage raɗaɗin wannan cuta. Senegal: Zaɓen da aka kammala. North Korea: Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin sake zama da Amurka bayan tashi taron birnin Hanoi da aka yi ba tare da wata nasara ba. Amurka ta taya Najeriya murnar kammala zaɓe cikin kwanciyar hankali. Somalia: Wani harin ƙunar baƙin wake, ya salwantar da rayuka a ƙasar Somaliya.
ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

World Radio Day in Hausa (Ranar Rediyo ta Duniya 2019)

DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019)
Cikin shirin za a ji yadda wasu al'umomi ke bayyana muhimmancin kafar sadarwar rediyo a rayuwarsu ta yau da kullum, dai lokacin da ake ranar rediyo ta duniya. A Najeriya kuwa mazauna yankunan karkara ne ke damuwa da yawan alkawura da 'yan siyasa ke dauka ba tare da cikawa ba.
Host: Munta Gayuwa* Nigeria: Za mu ji yadda mazauna yankunan karkara a Najeria suke cewa suna cikin halin taƙaici na roman baka da 'yan siyasar ƙasar ke yi musu, tsawon shekaru da ƙasar ta kama mulki irin na demokraɗiya. Toh wane irin alƙauran ne wadannan 'yan siyasa ke yi wa wadannan mutane na karkara?"In mun ci zaɓe, za mu yi muku hanya. In mun ci zaɓe, za mu kawo muku wuta, asibiti, da sauran abubuwa. Amma ko ɗaya, ba wanda ya taɓa cika mana. Wani pole-waya an kafa a nan ya kai har shekara goma sha biyu (12), amma wallahi ba a zo yin komai ba!" Nigeria: Muna tafe da rahoto kan wannan matsala. Hakannan kuma za'a ji al'ummar Fulani da dokar hana kiwo ta shafa a jihar Benue da ke tsakiyar Najeriyar. Sun buƙaci kariya ne daga jami'an tsaro a duk inda suke don basu damar zaɓe kamar sauran 'yan ƙasar Najeriyar. World Radio Day 2019: Yayin kuma da ake ranar rediyo ta duniya, za mu ji yadda wasu al'ummomi ke bayyana mahimmancin kafarta sadarwa a garesu. Morocco: Hukumomi a ƙasar Morocco, sun kama wasu Faransawa da suka ce suna ɗaukar nauyin ƙungiyar nan ta IS. Nigeria: Mutane da dama sun mutu lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe na shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya. Thailand: Wasu fursunoni, wato 'yan ƙabilar Uyghir, sun tsere daga hannun jami'an tsaro a ƙasar Thailand.
BBC Hausa Shirin Hantsi (Wed Feb 13th 2019)

BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT)

BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG)

Kanun Labaran BBC Hausa Shirin Safe (Tue Feb 12th 2019 - 6:30am NG)

DW Hausa Shirin Safe 10.02.2019 Headlines
Za ku ji cewar kasar Turkiya tayi Allah wadai da irin cin zarafin da kabilar Uighur ke fuskanta a kasar Chaina
Host: Zulaiha Abubakar Kibiya African Union: Ƙungiyar tarayyar Afika ta AU, za ta gudanar da babban taron ta na kwanaki biyu a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha (Ethiopia) inda shugwabannin ƙasashen Afrika za su tattauna batun kwararar baƙin haure daga nahiyar zuwa ƙasashen turai. Daidai lokacin da a cigaba da lalubo dabarun warware rikicin addini da ƙabilanci da ke barazana da rayuwar al'umar Filato. Cibiyar sasanta tsakanin addinai mai ofishi a Kaduna, ya ƙaddamar da shirin yafewa juna tsakanin al'ummomin jihar bayan shafe sama da shekaru goma sha bakwai ana tashin hankali. Shugaba Paul Kagame zai sauka daga muƙaminsa a ƙungiyar AU. An shawarci sojojin ƙasar Venezuela a kan kayan agaji. Turkiyya ta yi Allah-wadai da cin zarafin da ƙabilar Uighur ke fuskanta China.
BBC Hausa Shirin Hantsi 10/02/2019
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin Turkey, China: Turkiyya ta buƙaci ƙasar Sin da ta gaggauta ta rufe sansanonin da take tsare musulmi 'yan ƙabilar Uyghur. UK: Yarima Philip na Birtaniya ya ajiye lasisinsa na tuƙi. Nigeria's corn farmers: Manoma masara sun bayyana irin yabon da suka ce sun samu a noman bara.Mun samu cigaba wajen bunƙasuwan masara daga shekara ta dubu biyar da sha biyar zuwa yanzu (2015-present). Da, masarar da ake nomawa a wannan lokaci ba ta wuce tonne miliyan sha biyar ba. Amma yanzu zuwa bana, noman da aka yi na bara shekara ta dubu biyu da sha takwas (2018), an noma ta miliyan ashirin. Shirin Mu Tattauna.
BBC Hausa Shirin Safe 10/02/2019
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin Nigeria Elections 2019 / Zaɓe 2019: APC! APC! Today I want to teach Atiku a lesson.--Uban jam'iyyar APC Bola Ahmed Tunibu a yayin yaƙin neman zaɓen jihar Lagos ya ke cewa yau zan koyawa Atiku darasi. Za mu ji me yayi zafi da kuma yadda yaƙin neman zaɓen ya kasance. Sokoto Governor Debate: A yau BBC ke cika alƙawarinta na kawo muku mahawara tsakanin 'yan takaran gwamnan Sokoto. Africa: Shugwabannin ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Afrika za su soma wani taro da zai mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi nahiyar su.
BBC Hausa Shirin Yamma 09/02/2019
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Hosts: Ibrahim Mijinyawa Nigeria Elections 2019: Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP (the major opposition party), ta yi zargin cewa an hana ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a Abuja.Har mun tura mutanen mu waɗanda za su je su shiya mana wurin tsayawa a yi magana (podium)... sai aka ce musu wannan wuri ba za a ba mu shi ba. Don haka sai dai mu nemi wani. Chad: Rundunar sojin Cadi kuwa, ta ce ta kama 'yan tawaye da dama da suka tsallaka cikin ƙasar daga kudancin Libya bayan artabun da aka yi da su a arewacin ƙasar. Ethiopia: Tsofaffin 'yan tawaye ne sama da dubu guda suka miƙa da makamansu bayan wata yarjejeniya da aka ƙulla da su da gwamnatin ƙasar.
Pars Hausa Sunday, Feb 10th 2019

BBC Hausa - Shirin Rana na 07.02.2019
Host: Sulaiman Ibrahim Katsina

DW Hausa - Shirin Safe na 07.02.2019
A cikin shirin za a sha labaran duniya da kuma rahotanni kan zaben Najeriya da rikicin kasar Kamaru na 'yan aware da ke kara kamari. [5]
Hosts: Ramatu Garba Baba Nigeria Elections 2019: Za mu duba yanda/yadda 'yan takara ke cigaba da bayyana hanyoyin da za su bi don ɓullowamahimmam buƙatun al'ummar ƙasa. Ga kadan daga ra'ayoyin jama'an ƙasa kan abinda ya fi ci musu tuwo a ƙwarya[6]: Abubuwan da suka dawo yanzu tsakanin
Buhari's UN Speech 2017-9-19

Kanun Labaran Hausa 2017-9-5
